Informações:
Sinopse
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan alamurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi alumma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Episódios
-
An ci mutunci da zage-zage a Siyasar Amurka
31/10/2016 Duração: 20minShirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne akan dambarwar siyasar Amurka inda ya rage kwanaki a kada kuri’ar zaben shugaban kasa. A cikin shirin za a ji yanayin zaben Amurka da kuma yadda zaben na bana ya zo da sabbin abubuwa da ake ganin sun sabawa demokuradiyar kasar.
-
Jihohin da Abacha ya kirkiro sun yi shekaru 20
15/10/2016 Duração: 20minShirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da bikin cika shekaru 20 da jihohi 6 suka gudanar wadanda Marigayi Janar Sani Abacha ya kirkiro a shekarar 1996. Shirin ya mayar da hankali a Jihohin Gombe da Zamfara. Shin kwanliya ta biya kudin sabulu? Sannan shirin ya tabo muhawarar da ake a Majalisar Dattijai kan wani kudirin doka na Daidaiton jinsi wato kudirin doka da zai ba mata damar yin kafada da kafada da maza wanda ke yin karo da addini.
-
Shirin Zabe a Ghana
09/10/2016 Duração: 20minShirin Dandalin Siyasa ya yi nazari kan shirin babban zaben kasar Ghana da za a gudanar a watan Disemba. Shirin kuma ya leka Najeriya game da batun fasa kwan da Hon Abdulmumin Jibril ke yi a Majalisar dokokin kasar.