Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 3:45:18
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episódios

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwan da ke musu tuwo a ƙwarya

    28/11/2025 Duração: 08min

    Yau Juma'a kamar kowanne mako, muna baku damar tofa al'barkacin bakinku kan batutuwan da ke ci muku tuwo a kwarya, cikin shirin ra;ayoyin ku masu sauraro. Danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan ɗaukar sabbin 'yansanda dubu 30 a Najeriya

    25/11/2025 Duração: 10min

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin janye dubban ƴansanda da ke kare manyan mutane a sassan ƙasar, tare da ta sanar da shirin ɗibar wasu sabbin ƴansanda kusan dubu 30 don tunkarar matsalar tsaro da ta addabin ƙasar. Shin ko wace irin gudunmuwa hakan zai bayar a ƙoƙarin tunkarar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fama da shi yanzu haka? Wannan shi ne maudu'in da  muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan ta'azzarar matsalolin tsaro a Najeriya

    24/11/2025 Duração: 09min

    A Najeriya, ƴan bindiga masu gurkuwa da mutane domin ƙarbar ƙudin fansa, sun tsananta kai hare-hare makarantu tare da sace ɗaibai a baya-bayan nan, lamarin da ya sa gwamnatoci a wasu jihohin ƙasar suka ɗauki matakin rufe makarantu a matakai daban-daban. Hakan ya biyo bayan sace dalibai a jihohin Kebbi da Neja a makon da ya gabata, lamarin da ya sake haifar da fargaba kan tsaron dalibai da makarantu da kuma makomar ilimi a yankin arewacin Najeriya. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin...

página 2 de 2