Wasanni

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 3:59:25
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Episódios

  • Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa ke baiwa ƙwallon Ƙafa a Najeriya

    06/10/2025 Duração: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci za yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon Ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Najeriya. A wani bangare na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon kafa a Nigeria, ɗai-ɗaikun jama’a da ƴan kasuwa kai harma da tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles ta ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon ƙafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira FOOTBALL ACADEMY, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..

  • Mahangar masana game da yadda Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana

    29/09/2025 Duração: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali kan yadda ɗan wasan gaba na PSG ɗan Faransa Ousmane Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or a bana, bayan nasarar shi ta lashe kofuna da dama cikin kakar da ta gabata da ƙungiyar tasa da ke birnin Paris. Duk da cewa anjima ana hasashen Dembele ya lashe wannan kyauta lura da namijin ƙoƙarinsa a kakar da ta gabata, amma wasu na da ra'ayin cewa sam ɗan wasan bai cancanci wannan kyauta ba. Game da wannan saɓanin ra'ayi, shirin na Duniyar Wasanni ya tattauna da masana a fagen na wasanni waɗanda suka bayyana ra'ayoyinsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Adawar magoya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙarawa gasar armashi

    22/09/2025 Duração: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya yi duba ne kan yadda adawar magoya bayan ƙungiyoyi ke karawa kwallon ƙafa tagomashi. Wasanni da dama ne dai ke samu karbuwa a duniya da suka haɗa da kwallon ƙafa da kwallon kwando da kwallon Cricket da Tennis da dai sauransu, amma kuma kowane  wasa na da irin nashi magoya baya da suke matuƙar ƙaunarsa da so a duniya. Bincike ya  nuna cewa babu wani wasa da ta fi kwallon kafa magoya baya a duniya, inda aƙalla mutane biliyan 3 da rabi ne ke sha'awar wasan baya ga ƴan kwallon kansu da suka kai miliyan 250, waɗanda hukumomin kwallon ƙafa a duniya FIFA ta yiwa rijista. Hatta a Najeriya nuna sha'awa na magoya baya ba ya misaltuwa, domin babu lungu da sako da wasan bai samu karɓuwa ba  musamman ma wasannin nahiyar Turai da ya fi can hankali. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Makomar tawagar Najeriya a ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar lashe kofin duniya

    15/09/2025 Duração: 09min

    Shirin a wanan mako tare Khamis Saleh, ya yi duba ne kan makomar tawagar Najeriya a ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar lashe kofin duniya, inda a tsakiyar makon da ya gabata aka kammala wasannin na 8 na sharen fagen zuwa gasar lashe kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka za su karɓi bakunci a shekara mai zuwa. Kawo yanzu dai wasanni sun ɗauki zafi ganin cewa wasu daga cikin tawagogin ƙasashen sun fara jin kanshin halartar gasar, amma kuma wasu har yanzu tana ƙasa tana dabo. Latsa alamar sauri domin sauraron cikakken shirin.....

página 2 de 2