Al'adun Gargajiya

Yadda al'adar auren Zaga ke shudewa tsakanin kabilar Sayawa a Najeriya

Informações:

Sinopse

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda auren Zaga tsakanin al'ummar Sayawa ke komawa tarihi, salon al'adar da ke bayar da damar gadon mace ko kuma bayar da kyautar ta da sunan aure. Duk da tarin kabilun da ake da su a cikin jihohin Najeriya, kowace kabila na da irin nau’o’in al’adunta na gargajiya a fannonin rayuwa dabam dabam.Al’adun kan bambanta ne ta fuskar tsarin zamantakewa, ko ta fuskar auratayya da makamantarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....