Al'adun Gargajiya

Yadda sana'ar ƙira ke gushewar a al'adar ƙasar Hausa

Informações:

Sinopse

A yau shirin za ya kai mu Jamhuriyar Nijar, musaman jihar Maradi.A wannan yankin na Maradi a garin Radi, zamu duba batun kirar gargajiya da ke kan hanyar bacewa, bayan a can baya kira, wanzamci, sun kasance sana’o’i biyu da ake alfahari da su a cikin gari. A dauri, makeri baya noma a irin wannan lokaci na damina, sai dai ya yi ta aikin kera kayan noma da gyaransu idan sun lalace, idan kaka ta yi dukan manoma sai su hada masa dammuna hatsi, irin su dawa ko ma wake da zai kula da iyalinsa.