Bakonmu A Yau

Attahiru Bafarawa kan tsare yaran arewacin Najeriya saboda zanga zanga

Informações:

Sinopse

Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya tare da wasu ƙungiyoyin kare hakkin Bil Adama da kuma wasu fitattun ƴan ƙasar sun bayyana damuwa dangane da yadda rundunar ƴan sandan ƙasar ta gurfanar da wasu yaran da suka fita hayyacinsu a gaban kotu, inda ake tuhumarsu da zanga zangar neman kifar da gwamnati. Rahotanni sun ce ministan shari’a ya bukaci mika masa takardun shari’ar wadda ta haifar da cece kuce a fadin ƙasar. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ɗaya daga cikin dattawan arewacin Najeriya, kuma tsohon Gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.