Al'adun Gargajiya

UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundinta na al’adun duniya

Informações:

Sinopse

Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al’adun duniya.Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al’adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa.  Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........