Bakonmu A Yau

Amb Abubakar Cika kan mataki AES na zaman rundunonin sojinsu cikin shirin ko ta kwana

Informações:

Sinopse

Ƙasashen AES da suka haɗa da Nijar, Mali da kuma Burkina Faso sun yi watsi da ƙarin wa’adin watanni shidda da ECOWAS ta yi musu a makon jiya, kan lokacin ficewarsu daga cikin ƙungiyar a hukumance, rangwamen da zai fara aiki a watan Janairun dake tafe. Cikin sanarwar da suka fitar, ƙasashen uku sun sanar da baiwa rundunonin sojinsu umarnin zama cikin shirin kar ta kwana. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Ambassada Abubakar Cika tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu..................