Bakonmu A Yau

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 1:29:14
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episódios

  • Babu wanda muka kora daga sansanin ƴan gudun hijira - Babagana Umara Zulum

    19/09/2024 Duração: 03min

    A karon farko bayan gagarumar ambaliyar da ta shafi birnin Maiduguri, Gwamnan Jihar Babagana Umaara Zulum ya bayyana girmar matsalar da kuma kokarin da suke wajen tinkarar ta a hira ta musamman da RFI Hausa. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawarsu da Ahmed Abba wanda yanzu haka ke birnin na Maiduguri.....

  • Gwamnatin jihar Borno ta bukaci al'umar birnin Maiduguri dasu kiyaye abinda zasu ci ko su sha

    18/09/2024 Duração: 03min

    Gwamnatin Jihar Barno da ke Najeriya ta gargadi mazauna birnin Maiduguri da su kaucewa cin kayan abinci da ruwan shan da aka dauko daga yankunan da aka samu ambaliya, domin samun kariya. Hukumomin sun ce wadannan kayayyaki na dauke da sinadarin dake fita daga gawarwaki da masai da wasu na dabam da ka iya haifar da cututtuka. Dangane da wannan gargadi Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jmai'ar Ahmadu Bello dake Zaria,kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Sai a latsa alamar sauti damin samun cikakken shirin.

  • Dr Aliyu Dala kan ambaliyar da ta mamaye akasarin birnin Maiduguri

    17/09/2024 Duração: 03min

    Wani masani ɗan jihar Bornon Najeriya Dr Aliyu Dala ya danganta ambaliyar da ta mamaye akasarin birnin Maiduguri da sakacin jami'an gwamnati. Dr Dala wanda ke cikin ƙungiyar ƙwararrun ƴan Arewacin Najeriya mazauna Turai ya ce sun yi nazari akan matsalar ambaliyar kuma sun gabatar da rahoto a kan matakan da ya dace a dauka, cikin su harda na Maiduguri amma babu abinda aka yi a kai. Ku latsa alamar sauti don jin yadda tattaunawarsu ta gudana da Bashir Ibrahim Idris.....

  • Sheikh Mansur Ibrahim a kan Maulidi

    16/09/2024 Duração: 03min

    Al’ummar musulmi a sassan duniya na gudanar da bukukuwan Mauludi, domin tunawa da ranar da aka haifi annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah.To domin sanin muhimmancin wannan rana ga musulmi, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Sheikh Mansur Ibrahim da ke garin Kaduna a Najeriya.

  • Attahiru Bafarawa: Rashin haɗin kai tsakanin dattawan arewa

    12/09/2024 Duração: 03min

    A Najeriya, ga alamu ba dukannin mutanen Arewacin ƙasar ne suka yarda da irin rawar ƙungiyar Dattawan yankin wato Arewa Consultative Forum ke takawa don haɗa kan jama’a da kuma kare muradun alummar yankin ba. Tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar ta ACF, ya zargin magabatan ƙungiyar da nuna gazawa a cikin aikinsu. Ga dai abin da ya shaida wa Bashir Ibrahim Idris.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu

  • Tattaunawa da Dr Moussa Hassan Ousseini kan taron sauyin yanayi a Nijar

    11/09/2024 Duração: 03min

    Kwararru game da matsalar sauyin yanayi da kuma wakilan gwamnatoci da na ƙungiyoyi, sun fara gudanar da wani taron kwanaki uku a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, domin tattauna matsalar sauyin yanayi a Yankin Sahel da kuma Yammacin Afirka. To domin jin muhimmancin wannan taro, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Moussa Hassan Ousseini, jagoran ƙungiyar Jeunes volontaires pour l’environnement du Niger mai rajin kare muhalli a Jamhuriyar Nijar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.....

  • Kwamrade Audu Titus Amba game da hare-hare ta'addanci kan dalibai da makarantu

    10/09/2024 Duração: 03min

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta koka kan yadda aka samu ƙaruwar kashi 20 cikin 100 kan hare-haren da ake kai wa makarantu da sauran cibiyoyin ilimi da kuma ɗalibai a tsakanin shekarun 2022 zuwa 2023 da ta gabata, musamman a ƙasashen da yaƙi ya ɗaiɗaita. Cikin rahoton da ta fitar, hukumar kula ilimi, da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta ce sau dubu 6,000 aka kai wa dalibai da malamansu da kuma cibiyoyin ilimi hari, ciki har da hare-hare dubu 1,000 inda sojoji ke mayarda makarantun sansani. Ganin cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen makarantu da dama ke fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci ya sa Nura Ado Suleiman tattauna wa da Kwamrade Audu Titus Amba, shugaban ƙungiyar malaman Najeriyar.

  • Alhaji Shehu Yaro Jimoh: Kan tsadar rayuwa a Najeriya

    06/09/2024 Duração: 03min

    Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa a Najeriya, manazarta na ganin cewa ba wata hanya da za ta taimaka domin kawo wa jama’a sauƙi face bayar da damar shigar da kayan abinci da na masarufi daga ƙetare har zuwa cikin ƙasar har zuwa lokacin da lamurra za su daidaita. Alhaji Shehu Yaro Abdulkadir Jimoh, ɗan kasuwa ne kuma shugaban al’umma, na daga cikin masu goyon bayan wannan shawara, ga kuma abin da yake cewa a zantawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu

  • Alhaji Bashir Dalhatu kan matsalolin tsaro a yankin Arewacin Najeriya

    05/09/2024 Duração: 03min

    Shugaban majalisar gudanarwar Kungiyar tintiba ta arewacin Najeriya wato ACF, Alhaji Bashir Dalhatu ya nemi gafarar 'yan arewacin kasar saboda abinda ya kira gazawar su ta kare yankin daga fadawa rikici mafi muni a tarihinsa. Dalhatu ya ce suna ci gaba da lalubo hanyar shawo kan wadannan matsaloli da suka yiwa yankin kamun kazar kuku. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu tare da Bashir Ibrahim Idris.......

  • Hon Samaila Muhammed kan karin farashin man fetur a Najeriya

    04/09/2024 Duração: 03min

    Kamfanin man NNPC a Najeriya ya sanar da kara farashin mansa bayan ƙwashe ƙwanaki ana shan wahalar samum man da kuma tsadarsa. Farashin man yanzu ya kai kusan naira 900 a Lagos, ya yin da ya haura dubu guda a arewacin kasar. Dangane da karin farashin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arzikin ƙasa kuma tsohon ɗan majalisar tarayya Hon Samaila Muhammed, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu........

  • Abdul'aziz Abdul'aziz kan karancin man fetur a Najeriya

    03/09/2024 Duração: 03min

    Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin ci gaba da wadata 'yan kasar da man fetur, biyo bayan karancin sa da aka saba gani bayan ikirarin kamfanin mai na NNPC na cewa bashi ya yi masa katutu. Babban mai taimakawa shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Abdul'aziz Abdul'aziz ne ya bayyana hakan ya wata ziyara da ya kawo Ofishin RFIDanna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar tare da Micheal Kuduson.

  • Aliyu Dahiru Aliyu kan yadda ƴan ta'adda ke amfani da dandalin sada zumunta

    02/09/2024 Duração: 03min

    Wani bincike da  Jaridar  Human Angle ta gudanar ya bayyana yadda 'yan ta'adda ke amfani da kafofin sada zumunta domin yada manufofinsu da kuma yaudarar matasa suna shiga cikin su. Ko a baya bayan nan an ga wani daga cikinsu yana rike da tarin kudi da kuma bindiga, inda ya bukaci jama'a su tura lambar ajiyar bankinsu domin aike musu da kudin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Mataimakin Editan Jaridar Aliyu Dahiru Aliyu dangane da binciken na su, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

  • Tattaunawa da Malam Sani Rufa'i kan sabuwar dokar tube rigar ɗan kasa a Nijar

    30/08/2024 Duração: 03min

    Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta amince da wata dokar tube rigar ɗan kasa a kan duk wanda aka samu da aikata laifuffukan ta'addanci ko kuma taimakawa masu ta'addanci. Dokar ta kuma shafi masu yiwa kasa zagon kasa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Sani Rufai a kan sabuwar dokar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana

  • Dakta Ahmad Tijjani Lawal kan alaƙar Morocco da sauran ƙasashen Afrika

    28/08/2024 Duração: 03min

    Kasar Morocco ta tashi tsaye wajen kulla alaka ta kusa da sauran takwarorinta na nahiyar Afirka musamman ma kasashen da suke cikin ECOWAS, kungiyar da shekarun baya bayan nan Moroccon ta nemi a bata damar shiga cikinta. Yunkurin na Morocco na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke samun cigaba a fannoni da dama da suka hada da noma, samar da makamashi da kuma tattalin arziki.Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Ahmad Tijjani Lawal fashin baki kan lamurran kasa da Kasa dake Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Wane hali ake ciki game da shigar da kayan abinci masu rahusa Najeriya

    27/08/2024 Duração: 03min

    Kusan watanni 2 da bada umarnin shigar da abinci Najeriya ba tare da kudin fito ko haraji ba domin karya farashinsa da kuma wadata jama'a, amma har yanzu samar da abincin ya gagara. Rahotanni sun ce 'yan kasuwa sun kasa samun kudaden kasashen ketare domin sayo abincin daga kasashen duniya. Sanata Garba Musa Mai Doki, dan majalisar dattawa daga jihar Kebbi ya ce ya zama dole gwamnati ta shigo da abincin da kanta domin wadata jama'a da kuma rage musu radadin halin da suke ciki.Ga yadda tattaunawarsu ta gudana da Bashir Ibrahim Idris lokacin da ya ziyarci ofishinmu a Lagos.

  • Dokta Kamilu Rangaza a kan ranar Hausa ta 2024

    26/08/2024 Duração: 03min

    Ranar 26 ga watan Augusta rana ce ta bikin harshen Hausa ta duniya, an fara gudanar da bikin ne a shekarar 2015, kuma kasashen Nigeria, Niger, Chad, Ghana, Mali, Senegal, da sauran su na sahun gaba wajan gudanar da bikinAisha Shehu Kabara ta tattauna da Dakta Kamilu Bashir Rangaza, Malami a sashen koyar da harshen hausa na kwalejin Aminu Kano dake tarayyar  Najeriya

  • Tattaunawa da Adamu Ɗansitta kan mummunar ambaliyar ruwa a Jigawa

    21/08/2024 Duração: 03min

    Hukumomi a Jihar Jigawa da ke Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 30, yayin da daruruwan gonaki da gidaje suka lalace sakamakon ambaliyar ruwan da ta yi wa jihar illa. Dangane da wannan iftila'i Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Muhammd Ahmad Adamu Dansitta, mai bayar wa gwamnan jihar shawara ta musamman.Ku latsa alamar sauti domin jin cikakkakiyar hirar da suka yi.

  • Ibrahim Garba Wala kan tallafin man da Najeriya ta zuba na tiriliyan 7

    20/08/2024 Duração: 03min

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta biya kusan naira tiriliyan 7 a matsayin tallafin man fetur a wani yunƙuri na ganin al'ummar ƙasar basu sayi man da tsada ba.  A cewar Gwamnatin namijin ƙoƙarin da ta yi wajen zuba wannan maƙuden kuɗaɗe su ne suka taimaka wajen hana hauhawar farashin man na fetur ta yadda har ta kai ana iya sayen man da sauƙi a yanzu.Sanarwar da gwamnatin Najeriyar ta fitar ta ce ta sanya wannan tallafi ne daga watan Agustan bara zuwa Disambar shekarar nan.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ibrahim Garba Wala ɗaya daga cikin masu fafutukar kare haƙƙin jama'a a ƙasar ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.

  • Tattaunawa Sanata Garba Musa Mai Doki kan matsalolin ƴan bindiga a Kebbi

    19/08/2024 Duração: 03min

    Mazauna yankin arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da bayyana irin ƙuncin rayuwar da suka samu kansu a sakamakon yadda ƴan nbindiga suka kassara yankunan na su ta hanyar hare-hare da garkuwa da mutane wanda ya tilastawa al'ummomin wasu garuruwan barin matsugunansu baki daya.  A ƙarshen makon da ya gabata ne Sanata Garba Musa Mai Doki da ke wakiltar jihar Kebbi ya ziyarci ofishinmu inda suka tattauna da Bashir Ibrahim Idris dangane da halin da suke ciki, ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Ahaji Umaru Dembo kan bukatar Ɗangote da wasu matatun mai na Najeriya

    14/08/2024 Duração: 03min

    Katafariyar matatar man Ɗangote ta ce ita da wasu masu tace mai na cikin gida na bukatar akalla ganga dubu 600 na ɗanyen mai kowacce rana domin gudanar da ayyukansu, yayin da ƙasar ke samar da ganga miliyan guda da dubu 300 kowacce rana. Sai dai ga alama har yanzu matatun ba su kai ga samun biyan bukata ba, dole sai sun dogara ga wadanda suke shigo da shi daga kasashen ketare. Dangane da wannan batu ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon ministan albarkatun mai Ahaji Umaru Dembo.Kuna iya latsa alamar sauti domin jin cikakkiyar hira da muka yi da shi.

página 1 de 2