Al'adun Gargajiya

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 4:00:23
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Episódios

  • Shirye-shirye na musamman kan tarihin zuwan Turawa ƙasar Hausa

    17/09/2024 Duração: 09min

    Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ci gaba ne game da jerin shirye-shiryen da muka faro kan zuwan Turawan mulkin mallaka zuwa ƙasar Hausa. Turawan sha mamakin abinda suka tarar, kasancewar sun samu al’ummar Hausawa da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauran harkoki na rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare ta Abdoulaye Issa.......

  • Jerin shirye-shirye kan tarihin zaman takewar ƙasar Hausa kafin zuwan Turawa

    10/09/2024 Duração: 09min

    Shirin a wannan makon ya maida hankali ne yadda tsarin shugabanci ya ke a kasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........

  • Yaya tsarin tafiyar da mulki yake a ƙasar Hausa kafin zuwan turawa

    27/08/2024 Duração: 09min

    Shirin na wannan mako ya duba irin tasirin masu mulki a ƙasar Hausa kafin zuwan turawan Mulkin mallaka Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani

  • Yadda sana'ar ƙira ke gushewar a al'adar ƙasar Hausa

    13/08/2024 Duração: 09min

    A yau shirin za ya kai mu Jamhuriyar Nijar, musaman jihar Maradi.A wannan yankin na Maradi a garin Radi, zamu duba batun kirar gargajiya da ke kan hanyar bacewa, bayan a can baya kira, wanzamci, sun kasance sana’o’i biyu da ake alfahari da su a cikin gari. A dauri, makeri baya noma a irin wannan lokaci na damina, sai dai ya yi ta aikin kera kayan noma da gyaransu idan sun lalace, idan kaka ta yi dukan manoma sai su hada masa dammuna hatsi, irin su dawa ko ma wake da zai kula da iyalinsa.

  • Yadda Kabila Berum a Najeriya ke gudanar da bukukuwan su na al'ada

    30/07/2024 Duração: 09min

    A wanan makon shirin ya mayer da hankali ne kan yadda kabilar Berum da ke jihar Plateau ta tarayyar Najeriya ke gudanar da bukukuwan su na al'ada. Kuna iya latsa alamar sautin domin sauraren cikakken shirin.....

  • Shirin ya mayar da hankali kan Kabilar Gwari a Najeriya

    23/07/2024 Duração: 10min

    Shirin na wannan mako zai yi duba ne kan Kabilar Gwari da ake samun su a tsakiyar Najeriya. Kabilar Gwari da bahaushe ke kira da "Gwarawa" na da al'adu daban-daban masu ban mamaki da suka sha banban da sauran kabilun mutanen da ke kewaye da su.Domin jin cikakken shirin dannan alamar saurare tare da Abdullahi Isa

  • Shirin yayi waiwaye kan rayuwar fitaccen makadin gargajiya marigayi Alhaji Ali na Maliki

    09/07/2024 Duração: 09min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan rayuwar fitaccen mawakin gargajiya na jamhuriyar Nijar Alhaji Ali na Maliki Mawakin haifafffen kauyen Sarkin arewa dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar  ya kwashe shekaru akalla 80 na rayuwar sa yana taka rawa a fagen na raye-raye da kade-kaden gargajiya.Shirin ya kuma yi waiwaye kan rayuwar mamacin da ya bar yara 23 a duniya, kuma cikin su guda ya gaje shi.Dannna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abduoullaye Issa. 

  • Yadda al'ummar Wemawe na Benin ke shirya bikin al'adunsu a duk shekara

    02/07/2024 Duração: 09min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako, ya je jamhuriyar Benin musaman yankin Wemewe, inda ƙabilar yankin ke shirya wani ƙasaitaccen bikin nuna al’adunsu a duk shekara, wadda ke ƙarfafa danƙon zumunci tsakaninsu da sauren ƙabilu. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...

  • Irin rawar da masarautu ke takawa wajen kawo sauye-sauyen da suka kamata kashi na 2

    11/06/2024 Duração: 09min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ci gaba ne akan na makon daya gabata wanda ya duba muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. inda shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........

  • Irin rawar da ya kamata masarautu su taka wajen kawo sauye-sauyen da suka kamata

    04/06/2024 Duração: 10min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........

  • Koken Jama'a a kan yadda hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi rikon sakainar kashi

    21/05/2024 Duração: 10min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda Jama'a ke koken game da rikon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi, kamar Makon jiya yau ma shirin ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da shugaban kwamitin raya Al'adun Gargajiya na Majalisar dokokin Jihar, Hon. Sarki Aliyu Daneji.Ku latsa alamar sauti don jin yadda shirin ya kasance....

  • Yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Kano da ke Najeriya

    14/05/2024 Duração: 10min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi.Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata.

  • Yadda tsadar rayuwa ke barzana ga Maroka da Sankira a Jamhuriyar Nijar

    26/03/2024 Duração: 10min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar. Akwai mu dauke da yadda Maroka da kuma Sankira ke fuskantar barazana a sakamakon tsadar rayuwa.Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.

  • Yadda masarautar Hausawan Turai ke gudanar da ayyukanta

    19/03/2024 Duração: 10min

    Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........

  • Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu

    05/03/2024 Duração: 10min

    A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976,  aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah  da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.  Amma yayinda gwamnatin Nigeria ke tunanin sake damka wa Sarakuna wannan dama, wasu daga cikin su fara bijiro da sabbin matakai da nufin tsare rayuka da dukiyar al’ummarsu daga ‘yan ta’adda.A baya bayan nan, Mai Martaba Sarkin Ningi a jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad ‘Danyaya, ya samar da wata katafariyar kungiyar tsaro ta ‘yan sa-kai, wacce ke karade sako da lungun yankin don yaki da miyagun iri.

  • Yadda kananan kabilu suka samu wakilci a masarautar Katsinar Maradi

    27/02/2024 Duração: 09min

    Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al’ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al’adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa.  Masarautar Katsinar Maradi dai yanzu ta zama madubi kuma abin koyi  a bangaren hadin kan al'ummar Nijar.

  • Shiri na musamman kan marigayi Salissou Hamissou

    20/02/2024 Duração: 10min

    Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon na musamman ne, wanda ya yi duba akan irin gudunmuwar da marigayi Salissou Hamissou ya bayar a bangaren al'adu, musamman a lokacin da ya ke gabatar da wannan shiri na Al'adunmu na gado.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.....

  • Yadda al'adar auren Zaga ke shudewa tsakanin kabilar Sayawa a Najeriya

    13/02/2024 Duração: 09min

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda auren Zaga tsakanin al'ummar Sayawa ke komawa tarihi, salon al'adar da ke bayar da damar gadon mace ko kuma bayar da kyautar ta da sunan aure. Duk da tarin kabilun da ake da su a cikin jihohin Najeriya, kowace kabila na da irin nau’o’in al’adunta na gargajiya a fannonin rayuwa dabam dabam.Al’adun kan bambanta ne ta fuskar tsarin zamantakewa, ko ta fuskar auratayya da makamantarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....

  • Yadda wasu abincin gargajiya na bahaushe ke barazanar bacewa

    12/12/2023 Duração: 10min

    Shirin al'adunmu na gado na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda abinci gargajiya irin na Bahaushe ke bata sannu a hankali Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa

  • Yadda sana'ar rini ke bacewa sannu a hankali a arewacin Najeriya

    14/11/2023 Duração: 10min

    Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Issa ya maida hankali ne kan bacewar sanar gargajiya ta rini a jihar Kano dake arewacin Najeriya, kafin daga bisa shirin ya leka Maradi dake jamhuriyar Nijar.

página 1 de 2